Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dubban 'Yan Gudun Hijira a Jihar Nasarawa Sun Koka da Rashin Tallafi daga Gwamnati


Gwamna Tanko Al-Makura na Jihar Nassarawa
Gwamna Tanko Al-Makura na Jihar Nassarawa

Tashe-tashen hankula da aka yi a jihar Nasarawa kwana kwanan nan ya haifar da dubban 'yan gudun hijira da suka gudu daga gidajensu sun bazu a sansanoni daban daban inda basa samun taimako daga gwamnati.

Tashe-tashen hankalin yayi sanadiyar rasa rayuka da dama tare da asarar dukiyoyi da dama.

'Yan gudun hijiran sun roki gwamnati da jama'a akan su kai masu dauki. Wani James yace an farmasu ne a kauyukansu shi yasa suka gudu zuwa inda suke yanzu. Inji James mayakan Fulani ne.

Wani Muhammed Garba yace sun ga maharan kawai sai suka gudu, sun bar garin sai maharan suka kama kone-kone. Yana zaton Mada ne suka zo. Yace tun safe shi bai ci komi ba kuma babu wanda ya leko ya basu komi. Kawo 'yanzu basu san inda iyalansu suke ba.

Wata Lydia Sunday daga Atabula tace babu jami'an tsaro a kauyensu lokacin da maharan suka zo lamarin da yasa suka gudu kafin a kone gidajensu. Daji suka bi suka bulla wani garin. Basu da abinci yara kuma suna ta kuka. Tace ita da iyalinta babu abun da suka dauka. Suna hannun Allah amma suna rokon gwamnati ta dubesu da idon rahama.

Wani yace suna cikin damuwa matuka. Yace kungiyar Mbase ta kabilar Eggon ce ta kai masu hari. Su da yaransu basu da abun da zasu ci. Ko an shirya an dawo a zauna lafiya idan ba'a ja kunne Mbase ba zasu cigaba da yin abun da suka ga dama.

Gwamnan jihar Nasarawa Alhaji Umaru Tanko Al-Makura yace gwamnatinsa tana kokarin bada kariya wa jama'a. Abun da ya faru abun damuwa ne. Manufar gwamnati ita ce ta ba kowa kariya mutane su cigaba da rayuwarsu. Gwamnati zata magance tashin tashinar ta binciken musabbabin fitinar.

Gwamnan ya dora alhakin tashin hankali a jihar akan wasu 'yan siyasa wadanda suna da wata manufa daban domin su cimma muradunsu. Yace sun sansu domin sun kafa kwamitin bincike mai karfin kotu ta bankadosu. Gwamnati zata dauki matakan hukumtasu.

Ga rahoton Zainab Babaji.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:34 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG