A ranar Asabar, gwamnatin Sudan ta Kudu ta ki amincewa wani jirgi dauke da shugaban ‘yan tawaye Riek Machar ya sauka a Juba, babban birnin kasar, bayan da Machar ya bukaci shiga birnin da yawan dakaru da makaman da ba sa cikin matsyar da aka cimma a baya, a cewar Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Amurka, John Kirby.
Kirby ya kara da cewa, lokaci ya yi da bangarorin biyu za su kawar da duk wata matsala da za ta hana kafa gwamnatin hadakar, ta yadda shugaban ‘yan tawayen Riek Machar zai shiga birnin na Juba.
Ya kara da cewa har sai bangarorin biyu sun nuna shirinsu na sasantawa, kafin Amurka ta taimakawa Sudan ta Kudu wajen magance matsalolin tsaro da na tattalin arzikinta.