Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Aljanin “Jeni Cacer” Ya Bulla A Kwalejin Konni


Wasu dalibai
Wasu dalibai

An samu bullar wani al'amari da wasu ke cewa aljani ne tsaknin wasu dalibai mata a birnin Konni na Janhuriyar Nijar

An bayyana rahoton bayyana wani aljani a wata makarantar kwalejin mata a birnin Konni, wanda ake kira “Jeni Cacer,” wanda aka ce ya kan kama ‘yan mata a makarantun kwalejoji da sakandare. Hasali ma ance ranar Jumma’a da ta gabata, wanannan aljanin ya bulla a makarantar C.E. S ta birnin, inda dalibai mata suka rure da buge buge da faduwa mike tare da sa juna fitar da jinni, al’amarin da ya kawo tudu cikin makarantar.

Shugaban Makarantar Hassan Hani ya bayyana cewa a wani aji abin ya fara aukuwa sai kuma ya bazu. Y ace an taba samun bullar wannan aljani da dadewa. Ya ce wadan abin ya kai ga har sun yi ta buge-bugen juna sun kai ashirin ko ma fi.

Shugaban Makarantar ya yi kira ga daliban da su koma ga Allah a duk lokacin da abin ya faru da su. Ya ce wani sa’in da wuya a iya shawo kan daliban da aljanun su ka kama saboda su kan far ma duk wanda ya tunkare su.

Ga dai walkilinmu na birnin Konni Haruna Mamman Bako da cikakken rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:01 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG