Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsugune bata kare ba wa shugaban kasar Misra kan tsibiran da ya ba Saudiya kyauta


Shugaban Misra Abdel Fattah el-Sissi
Shugaban Misra Abdel Fattah el-Sissi

Ranar 15 ga wannan watan masu zanga zanga suka nuna fushinsu ga shugaban kasar Misra Abdel Fattah el-Sissi bisa ga kyautar da wasu tsibirai biyu wa Saudiya

Kodayake tsibiran biyu babu mutane dake zaune cikinsu masu zanga zangar sun lashi takobin cigaba yin zaman dirshen yau Litinin ranar tunawa da'yanto yankin Sinai.

Mahukuntan Misra sun riga sun kame 'yan gwagwarmaya da dama domin hana zanga zangar kin jinin gwamnati da aka shirya za'a yi yau kamar yadda wasu lauyoyi suka shaida tare da bayyana sunayen mutane 59 da gwamnatin ke tsare dasu. Mahukuntar kasar sun soma kame-kamen ne tun ranar Alhamis da ta gabata ta kai samame a wuraren shakatawa da gidajen mutane a birnin Alkahira.

A wani jawabi da ya yi ta kafar talibijan jiya Lahadi shugaban kasar Abdel Fattah el-Sissi ya kira 'yan kasar da su tashi tsaye su kare kasar daga wadanda ya kira masu aikata miyagun ayyuka. Yace dole "mu kare kasarmu. Ina sake jaddadawa misarawa cewa hakkin da ya rataya a kansu ke nan , wato su kare kasar su tabbatar da dorewarta" inji shugaban.

Jawabin nasa ka iya harzuka magoya bayan gwamnatinsa su fantsama cikin binin suna nasu zanga zangar lamarin da ka iya kaiga taho mu gama da 'yan adawa.

XS
SM
MD
LG