Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Bayyana Fushi Kan Zuga ‘Yan Kabilar Igbo Su Sa Guba A Abincin Yarbawa Da ‘Yan Benin


Members of the Lagos art and culture troupe perform during a parade celebrating Nigeria's 53rd year of independence from Britain in Ikeja district in Lagos October 1, 2013. Nigerian President Goodluck Jonathan on Tuesday promised a national dialogue to he
Members of the Lagos art and culture troupe perform during a parade celebrating Nigeria's 53rd year of independence from Britain in Ikeja district in Lagos October 1, 2013. Nigerian President Goodluck Jonathan on Tuesday promised a national dialogue to he

Al’ummar kudu maso gabashin Najeriya na ci gaba da bayyana fushi, kan kiran da wata mata mazauniyar kasar Kanada mai suna Amaka Patience Sunnberger ta yi, ga ‘yan kabilar Igbo da su fara sa guba a abincin Yarbawa da ‘yan kabilar Benin domin hallaka su.

A wani faifan bidiyo da aka sako a wannan mako ne aka ga matar, inda ta ke cewa a harshen Ingilishi, “Lokaci ya yi da za a fara sa wa Yarbawa da ‘yan Benin guba. Ku sa guba a duk abincinku a wurin aiki. Ku sa guba a ruwanku, don duk su mutu daya bayan daya.”

To sai dai kungiyar kare muradun kabilar Igbo ta Ohanaeze Ndigbo ta yi Allah wadai da al’amarin, tare da kira ga hukumomi da su gaggauta su taso keyar matar gida don ta fuskanci fushin doka.

A wata hira da sashen Hausa na Muryar Amurka jiya Alhamis, kakakin kungiyar Ohanaeze Ndigbo Dakta Alex Ogbonnia ya ce, “Hankali baya iya dauka cewar wani Igbo zai sa guba a abinci na jama’a saboda yin hakan na iya shafar kowa. Akwai ‘yan kabilar Igbo a ko’ina, kuma duk wani Igbo mai hankali bazai yi irin wannan mugun tunanin ba.”

Daga bisani Dakta Ogbonnia ya yi watsi da batun, tare da tabbatar wa Yarbawa da sauran kabilun Najeriya cewar kalamai daga irin wadannan masu shirin tayar da zaune tsaye baza su kasance wata barazana ga rayuwar al’ummar kasar ba.

A cewar wani shugaban al’umma Cif Damian Duru, “Wannan wani bala’i ne da ya fada wa kasar, kuma hakan ya sha faruwa ba tare da gwamnati ta dauki wani mataki ba. Manyan mutane a baya sun sha yin kalaman da suka fi na wannan matar muni kuma ba a dauki mataki ba. Ban ce ta aikata daidai ba. A hakikanin gaskiya so nake gwamnati ta seta misali da ita, ta kuma fito da tsari na yin maganin masu yin irin wadannan kalaman.”

“Irin wadannan kalamai abin Allah wadai ne, kuma yana da matukar muhimmanci a dauki mataki,” inji Chisom Igboko.

Haka shi ma wani mazaunin Benin babban birnin jihar Edo Barista Sani Muhammad Idris ya bayyana kin amincewa, inda ya ce, “Gaskiya ban goyi bayan kalaman nan ba. Kuma bazan goyi bayan duk kalaman da za su janyo husuma a gari ba saboda kalaman suna iya rusa kasar.”

Kazalika, Barista Mainasara Kogo Umar da ke sharhi kan lamuran yau da kullum ya tofa albarkacin bakinsa da cewa, “Kowa da kowa ya fito ya yi Allah wadai da irin wannan take-take da muke gani domin abubuwa ne wadanda idan aka yi wasa suna iya kawo mana matsala a kasar nan.”

Tuni majalisar wakilai ta Najeriya ta bukaci gwamnatin kasar Kanada ta gurfanar da Amaka Patience Sunnberger bisa zargin yin kalamai masu iza wutar kiyayya tsakanin kabilun kasar.

Karshe rahoton Alphonsus Okoroigwe.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG