Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Ce Rasha Ba Ta Da Hujar Koran Jami'an Diflosiyarta Su Sittin


Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka
Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka

Korar jami'an diflomasiyar Amurka daga Rasha tare da rufe karamin ofishin jakadancinta dake St Petersburg martani ne bisa abun da Amurka ta yiwa Rashan domin goyon bayan kasar Ingila

Amurka ta fada a jiya Alhamis cewa Rasha bata da hujjar korar jami’an diplomasiyar Amurka a zaman martanin kan korar jami'an Rasshar da Amurka da wasu kasashen yammacin duniya suka yi, saboda zarginta da amfani da makaman guba kan tsohon dan leken asirin Rashar dake zama a Ingila.


Fadar shugaban Amurka ta White House ta fitar da sanarwa da maraicen jiya Alhamis cewa abin da Rasha ta yi ya kara sukurkuta dagantakar Amurkan da Rasha.


Jami’ar harkokin diplomasiya da hulda da jama’a a ma’aikatar harkokin wajen Amurka Heather Nauert, ita ma ta yi Allah wadai da matakin na Moscow da ministan harkokin wajen Rashan Sergey Lavrov ya sanar da safiyar jiya.


Lavrov ya sanar da korar jami’an diplomasiyar Amurka guda sittin, a wani matakin mayar da martani a kan tasa keyar jami’an Rasha daidai wannan adadin da Amurka ta yi.


Haka kuma Rashan ta bada umarnin rufe karamin ofishin jakadancin Amurka na birnin Saint Petersburg, tana mai cewa tilas a tsaida aiki a wurin nan da kwanaki biyu.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG