Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ministan harkokin waje Rasha zai gana da shugabannin NATO


Sergei Lavrov ministan harkokin wajen kasar Rasha
Sergei Lavrov ministan harkokin wajen kasar Rasha

Ahalinda ake ciki kuma, yau Jumma’a ake sa ran ministan harkokin waje na Rasha Sergei Lavrov, zai gana da shugaban kungiyar tsaro ta NATO, Jens Stoltenberg, a wani taro da ake yi kan tsaro a birnin Munich na kasar Jamus, bayanda kungiyar tsaron kasashe da suke yammacin duniyan watau NATO ta bada sanarwar zata girke rundunar soja mafi girma a turai tun bayan kammala yakin duniya na biyu.

Amurka zata nunka har sau hudu kasafin kudaden da take kashewa a turai zuwa dala biliyan uku a shekara ta 2017, yayinda NATO ta kara yawan sojoji da zata rika horaswa da kuma za’a rika canji-canji, da samarda kayan yaki, sannan kuma kungiyar zata kafa rundunar ko-ta-kwana.

Rasha ta kira matakin na Turai a zaman barazana a turai.Kungiyar NATON tace matakin yunkuri na tabbatarwa kasashe da suke yankin wadanda suke bayyana damuwa kan take taken Rasha.

Rundunar sojojin Rasha ta shiga shirin ko ta kwana, kuma ta gudanar da atisayi na wani dan gajeren lokaci a tsakiya da kuma a kudancin Rasha kusa da Ukraine a yayinda ministocin NATO suka hallara a binrin Brussels cikin makon nan domin su tattauna kan matakai na kare kasashe da suke cikin kungiyar a gabashin Turai da kuma a yankin Baltic.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG