Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gobe Laraba Amurka Ke Makokin Tsohon Shugaba Bush


Shugaban Amurka Donald Trump da uwargidansa Melania Trump
Shugaban Amurka Donald Trump da uwargidansa Melania Trump

Shugaban Amurka Donald Trump ya ayyana ranar gobe Laraba a matsayin ranar makoki a Amurka, biyo bayan mutuwar tsohon shugaban kasa George H.W. Bush mai shekaru 94 a duniya.

Shugaban kasar Amurka na 41 wanda shi ya kawo karshen yakin cacar baki, ya kuma jagoranci yakin da ya tilastawa Sadam Hussein ficewa daga Kuwait a shekarar 1991.

Mutane biyu da suka yi aiki karkashin gwamnatinsa, tsohon sakataren harkokin wajen Amurka James Baker da tsohon sakataren tsaron Amurka kuma mataimakin shugaban kasa Dick Cheney, sun bayyana gidan talabijin na Fox News ranar Lahadi. Inda Baker ya bayyana Mista Bush a matsayin daya daga cikin shugabannin masu kyau da suka yi mulkin Amurka wa’adi daya tal.

Tsohon babban shugabannin hafsoshin soja kuma mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Colin Powell, ya ce shugaban kasar na 41, kuma matuki jirgin sama lokacin yakin duniya na biyu, ya san illar yaki don haka yake kokarin ganin baiyi amfani da sojoji ba a yakin Gulf na farko.

Jiya litinin aka ajiye gawar Bush a Majalisar Dokokin Amurka wadda zata kasance a can har zuwa gobe Laraba, inda za a gudanar da babbar karramawa ta kasa a majami’ar National Cathedral, kafin a mayar da gawarsa zuwa jihar Texas inda za a binneshi a ginin dakin karatunsa ranar Alhamis.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG