Amurka da China kasashe biyu mafi karfin tattalin arziki a fadin duniya, sun amince da a tsagaita wuta a fadan da ke tsakanin su na kasuwanci, an cimma wannan yarjejeniyar ne, bayan wata ganawa tsakanin shugabanin biyu Donald Trump da takwaransa Xi Jinging, bayan taron G20.
An samu tattaunawa mai ma’ana da kuma fatar zata kawo cigaba mai dorewa, a tsakanin kasashen biyu Amurka da China, a wani rubuttaccen bayani da shugaba Trump ya fitar, lokacin da yake kan hayarsa ta komawa gida Amurka, daga kasar Argentina a Jirgin Alfarma na Air Force One. Trump ya kara da cewar lallai wannan babbar karramawace gare shi, yayi aiki da shugaba Xi.
Ya kuma shaida wa ‘yan jarida dake cikin jirgin nasa cewar, “Wannan yarjejeniyace mai ma’ana, zan cigaba da rike jadawalin kudin fito, ita kuma China zata cire nata jadawalin" kuma zata dinga siyan kaya da yawa daga Amurka.”
Facebook Forum