Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amfani Da Na'urorin Zamani Zasu Taimaka Wajen Hana Magudin Zabe - Kwankwaso


Taron gangamin yakin neman zabe
Taron gangamin yakin neman zabe

A yayin da jam'iyyun siyasa ke ci gaba da yakin neman zabe a Najeriya jam'iyyar NNPP ta kaddamar da gangamin yakin neman zabe na Arewa maso yamma, inda dan takarar jam'iyyar Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bayyana gamsuwarsa da amfani da na'urorin da za su hana magudin zabe.

Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya ce abun da ke kara mai kwarin gwiwa game da zaben wannan shekarar shi ne amincewa da amfani da na'urorin da za su taimaka wajen hana magudin zabe.

Taron gangamin yakin neman zaben da kuma raba tutucin takarar gwamnoni da 'yan majalisa na shiyyar Arewa maso yammacin Najeriya da aka yi a Kaduna, ya samu halartar manyan Jam'iyyar kuma a wurin taron ne dan takarar shugaban kasa na Jam'iyyar NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya ja hankalin talakawan Najeriya game da wannan zabe da ke tafe.

Taron gangamin yakin neman zabe
Taron gangamin yakin neman zabe

Farfesa Rufa'i Ahmed Alkali, shi ne shugaban Jam'iyyar NNPP a Najeriya, ya ce al'uma su ne alkalan kansu game da halin da Najeriya ke ciki.

Shi kuwa jigon Jam'iyyar ta NNPP, malam Buba Galadima cewa ya yi al'umar yankin arewa maso yamma su shiga taitayinsu.

Taron gangamin yakin neman zabe
Taron gangamin yakin neman zabe

Ya zuwa yanzu dai manyan Jam'iyyun Najeriya uku ne suka yi irin wannan taron yakin neman zaben a jihar Kaduna, duk kuwa da cewa Jam'iyyun da suka tsaida 'yan takarar shugaban kasa sun haura goma.

Saurari rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00

XS
SM
MD
LG