Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hatsarin Kwale-Kwale Ya Hallaka Mutum 4 A Borno


Hatsarin kwale-kwale a jihar Kebbi
Hatsarin kwale-kwale a jihar Kebbi

Al’amarin ya hada da wani kwale-kwale dake dauke da fasinjoji wanda ya nutse a cikin ruwan ambaliya, abinda yayi sanadiyar mutuwar wasu mata 4.

Wani hatsarin kwale-kwale yayi sanadiyar mutuwar mutane 4 a garin Dikwa, na jihar Borno.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Borno, asp Nahum Daso yace sun samu rahotanni daga shelkwatar ‘yan sanda dake Dikwa cewar, wani hatsarin kwale-kwale ya afku a jiya Litinin da misalin karfe 3 da rabi na yamma a yankin Bakassi, tsakanin Mafa da Dikwa dake kan hanyar Maiduguri, dake jihar Borno.

Al’amarin ya hada da wani kwale-kwale dake dauki da fasinjoji wanda ya nutse a cikin ruwan ambaliya, abinda yayi sanadiyar mutuwar wasu mata 4.

Hatsarin ya hallaka mutane 4, dukkaninsu daga mazabar Bulabulin, dake Dikwa.

Ya bayyana sunayen wadanda hatsarin ya rutsa dasu da ya Mallum Shettima, babbar mace daga karamar hukumar Marte da Maimuna Akura, mai shekaru 10, da Umira Alhaji Bulama, ‘yar shekara 6 da kuma yagana Bulama Kawu, mai watanni 5 da haihuwa.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG