Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ambaliyar Ruwa Da Malalar Kasa Sun Hallaka Mutane 17 A California


Masu aikin gaggawa sun ceto wata mace a gidan da ya ruguje
Masu aikin gaggawa sun ceto wata mace a gidan da ya ruguje

Mutane goma sha bakwai suka rasa rayukansu da dama kuma suka bace bayan wani ambaliyar ruwa da malalar kasa a jihar California

Ambaliyar ruwa da malalar kasa sun hallaka mutane 17 baya ga gidaje da dama da su ka ruguza a arewacin birnin Los Angeles dake jihar California ta nan Amurka, inda a watan jiya wata wutar daji ta kokkona itatuwa da ganyayen da ke kan tsaunuka.

An bayar da rahoton cewa har ila yau akwai mutane akalla 17 da suka bace yayin da a jiya Laraba aka fadada binciken gano mutanen da abin ya shafa, bayan da wata babbar tawagar bincike da ceto ta iso daga Karamar Hukumar Los Angeles da ke kusa da wurin tare kuma da taimakon dogarawan tsaron gabar Amurka da wasu karin jami’an tsaron.

“Ba mu san inda su ke ba,” a cewar wata mai magana da yawun Karamar Hukumar Santa Barbara, Amber Anderson. “Muna jin sun salwanta wani wuri cikin baraguzan.”

Yanzu haka dai mummunan hadarin nan da ya janyo gocewar kasa da safiyar ranar Talata ya lafa, wanda hakan ya ba da dama ga masu kai daukin gaggawa da ke amfani da jirage masu saukar ungulu da karnuka don su ceto mutanen da su ka makale cikin gidajensu ko kuma su ka kafe cikin laka.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG