Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Uganda Zata Kaddamar Da Shafin Zumunta Na Yanar Gizo


Gwamnatin kasar Uganda, na yunkurin kirkiro shafufukan sada zumunta na yanar gizo, don gogayya da kamfanoni kamar su Facebook da Twitter. Jama’a da dama a kasar na sukar yunkurin na gwamnati.

Suna ganin cewar hakan zai dannen hakkin ‘yan kasar wajen bayyanar da ra’ayoyin su akan tsarin shugabancin kasar. Gwamnatin na ganin cewar manyan kamfanonin yanar gizo sai sunyi da gaske kafin su yi gogayya da shafin mallakar gwamnatin.

Ya zuwa yanzu gwamnatin bata bayyana sunan shafin ko kuma ranar da za’a kaddamar da shi ba. A cewar shugaban hukumar sadarwar kasar Uganda Mr. Godfrey Mutabazi, ya bayyana dalilin gwamnati na wannan yunkurin da cewar ‘yan kasar zasu samu damar bayyana ra’ayoyin su ga gwamnati dama duniya baki daya.

Basu da burin fito da wannan hanyar don muzgunawa ‘yan kasar, illa suna son amfani da damar domin ilmantar da ‘yan kasar da basu damar duk da ta dace.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG