Kwamishinar ta fadawa 'yan jarida cewa duk da tashin hankalin da ake fama da shi kusan kullum a jihar ta Borno, ana samun ci gaba a bangaren kiwon lafiyar jama'a.
Ta ce duk da irin wannan tashin hankalin, ana ci gaba da gudanar da ayyukan rigakafi a fadin jihar, yayin da dukkan cibiyoyin lafiya da asibitocin jihar su ma suke ci gaba da aiki a cewarta.
Kwamishinar ta klara da cewa gwamnatin jihar ta sayi motocin daukar marasa lafiya masu yawa wadanda ake amfani da su wajen gaggauta jigilar wadanda suka samu rauni zuwa asibiti domin ba su kulawar da ta kamata.