Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Loko Yayi Wa Sarki Sanusi II Kauye Da Yawa - Sarkin Loko


Tsohon Sarkin Kano, mai martaba Muhammadu Sanusi II
Tsohon Sarkin Kano, mai martaba Muhammadu Sanusi II

Bayan sauke sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II daga karagar mulki da gwamnatin Abullahi Ganduje ta yi a jiya, yanzu sarkin yana jihar Nasarawa inda zai yi zaman hijira.

Mai martaba sarkin Loko, Alhaji Abubakar Ahmad Sabo ya shaida wa wakiliyar mu Zainab Babaji cewa daga Kano aka kai sarkin zuwa karamar hukumar Loko inda zai zauna zuwa wani lokaci.

A cewarsa bai san tsawon lokacin da Sarki Sanusi II zai yi a Nasarawa ba, gwamnati ce zata yanke wannan hukuncin.

Ya ce "bai kamata a kawo sarki Sanusi nan ba, sabo da Loko ya yi kauye da yawa. A ganina ba zasu barshi ya dade a nan ba, kafin su canza masa waje."

Tun Jiya dai ‘yan Najeriya ke ta mayar da martani kan wannan batu da ya sami Sarki Sanusi II, inda da yawansu ke ta kokawa da lamarin, wasu kuma murna suke yi.

Wakiliyar mu Zainab Babaji ta yi kokarin jin ta bakin gwamnnatin Nasarawar amma bata same su ba saboda yanayin dare.

Saurari cikakken rahoton a sauti daga wakiliyar mu Zainab Babaji.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:20 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG