Biyo bayan sauke Muhammadu Sanusi Lamido na biyu daga sarautar jihar Kano tuni masu sharhi da dattawan Arewacin Najeriya suka fara tofa albarkacin bakinsu.
Tsohon Shugaban Najeriya Janar Abdulsalami Abubakar, wanda shine shugaban wani kwamitin sulhunta Sarki Muhammadu Sanusi da Gwamna Abdullahi Ganduje, da samar da zaman lafiya a Najeriya, ya bayyana cewa sun yi iya kokarinsu don ganin sun sasanta Sarki Sanusi da gwamnatin jihar Kano, amma abun ya ci tura.
A wata hira da Sashen Hausa, Janar Abdulsalami, ya ce duk da yake sun zauna a lokuta dabam dabam da gwamnan jihar Kano da kuma Sarki Muhammadu Sanusi na biyu, kafin suka yi wani zaman tare da su a lokaci daya, hakarsu mata cimma ruwa ba na neman a sasanta har ya kai ga sauke Sarkin, kasancewa gwamana ne mai wuka kuma mai nama.
Game da batun sa bakin Shugaba Muhammadu Buhari wajen sulhunta rashin jituwar, Janar Abdulsalami ya ce ba ya da masaniya ko shugaba Buhari ya sa baki ko a'a. Kuma in har ya sa baki, da mamaki a kai inda ake yanzu, ko da yake, a cewar Janar..
Ga cikakkiyar hirar cikin sauti.
Facebook Forum