Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Ta Kwaso ‘Yan kasarta 152 Da Suka Makale A Libya


Wasu 'yan Najeriya da suka makale a Libya
Wasu 'yan Najeriya da suka makale a Libya

Daruruwan dubban mutane ne ke zuwa kasar Libya da niyyar bi ta tekun Meditareniya mai cike hadari don tsallakawa zuwa kasashen turai.

Hukumar ba da agajin gaggawa ta kasa NEMA, ta karbi ‘yan Najeriya 152 da aka kwaso su daga kasar Libya.

Mutanen sun sauka ne a filin tashin jirage na Murtala Muhammad da ke birnin Legas a cewar Shugaban hukumar a shiyyar kudu maso yammacin Najeriya, Ibrahim Farinloye kamar yadda ya fada a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata.

Bayanai sun yi nuni da cewa ‘yan Najeriyar na daga cikin wadanda suka makale a kasar ta Libya wadanda suka je kasar a kokarinsu na ketara tekun Meditareniya don kai wa ga kasashen Turai.

Hukumar ta NEMA ta ce mutanen da aka kwaso tare da hadin gwiwar hukumar da ke kula da masu yin kaura ta kasa da kasa, sun hada da manyan mata 54, manyan maza da yara kanana 73.

Mutanen da aka kwaso sun nemi a mayar da su gida ne bisa radin kansu.

Daruruwan dubban mutane ne ake yaudara zuwa kasar Libya da niyyar bi ta tekun Meditareniya mai cike hadari don a tsallaka da su zuwa kasashen turai.

Bakin hauren kan bi ta kwale-kwale marasa inganci wajen yin tafiyar a teku, abin da kan kai ga mutuwar daruruwan mutane.

XS
SM
MD
LG