Hukumomi sun ce jirgin ya fadi ne kusa da karamin filin jirgin saman Boufarik, kimanin kilomita 25 daga kudu maso yammacin Algiers, babban birnin kasar, jim kadan bayan tashin shi.
Wadanda suka mutu sun hada da fasinjoji 247 da ma’aikatan jirgin guda 10.Yawancin wadanda suka mutu sojoji ne da ‘yan uwansu.
An kai gawarwakin asibitin sojoji na garin Ain Naddja don a tantance su, inji Ma’aikatar tsaron kasar.
Ma’aikatar tsaron ta kara da cewa jirgin yana da niyyar zuwa garin Tindouf ne da ke kudu maso gabashin Aljeriya.
Har yanzu dai ba’a san dalilin faduwar jirgin ba.
Facebook Forum