Jami’an tsaron Somalia sun ce sun kwace wasu makudan kudade a filin saukar jirage sama a Mogadishu daga birnin Abu Dhabi na kasar, Hadaddiyar Daular kasashen Larabawa, ko kum UAE atakaice.
Wasu manyan jami’an tsaro biyu sun shaidawa sashen Somaliyanci na Muryar Amurka cewa, an ajiye jakkuna uku da suke dauke da dala miliyon tara a babban bankin Somalia , ana gudanar da bincike a kansu.
Jakadan Daular kasashen Larabawan Mohammed Ahmed Othman Al-hammad, ya fadawa sashen Somalianci cewa, kudin ba na ofishin jakadanci ba ne. Yace kudi ne na ma’aikatar tsaron Somlia kuma zasu biya sojojin kasar albashin su.
Yace gwamnati na sane da zuwan wadannan kudade da za a baiwa sojoji tun kafin su zo. UAE tana horar da sojojin Somalia a Mogadishu da kuma kimanin yan sandan tsaron gabar teku dubu daya a yankin Putland
Jami’an Somalia sun hakikance cewa kudin ba na sojojin kasar ba ne. Albashin sojojin bai kai dala milyan daya ba, kuma wannan kuma sun kusan dala milyan 10, inji wani jami’i.
Dangantaka tsakanin Somalia da UAE tayi tsami tun shekarar da ta gabata, lokacin da gwamnatin Mohammed Abdullahi Mohammed ta ki amincewa da yanke hulda da Qatar kuma ta dauki matsayin ba ruwanmu a kan takaddama tsakanin Saudiya da Qatar.
Facebook Forum