Jamiyya mai mulki a kasar Aljeriya ta bukaci shugaba Abduazeez Boutiflika dattijo dan shekaru 81 da haihuwa da ya tsaya takarar shugabancin kasar zagaye na biyar duk ko da yake yana fama da cutar shanyewar jiki na tsawon shekaru.
Shugaban Jamiyyar ce ta FLN Djamel Ould Abbas shine ya bukaci Boutiflika da ya tsaya wannan takarar zagaye na biyar a cikin watan mayu na shekara mai zuwa.
Abbas dai yayi wannan maganar ce a jiya asabar lokacin da yake wa ’yan majilisar dokoki na jamiyyar jawabi, sai dai yace zabi na karshe ya rage ga shugaban.
Sau tari dai ba a faye ganin Boutiflika a bainar jamaa ba, domin abinda ba a sani ba har yanzu shin ko har yanzu shine ke tafiyar da mulkin kasar wacce tafi duk wata kasa girma a nahiyar Africa.
Abbas dai ya yaba da irin nasarorin da shugaban ya samu tun daga lokacin da yafara mulkin kasar a shekarar 1999, domin ko ya kawo wa kasar zaman lafiya bayan ta jima tana fama da yan taadda.
Kawo yanzu dai ba wani dan takara daya kunno kai, hakan ya biyo bayan jiran da suke yi ne na suji ko Boutiflika zai sake tsayawa takara ko a’a.
Facebook Forum