Kwanaki kadan bayan da ya dare kan karagar mulki, sabon Firai Ministan Ethiopia, ya fara cika alkawuran da ya dauka na samar da sauyi.
Cikin makon da ya gabata, hukumomin kasar sun rufe gidan yari “Maekelawi” da ya yi kaurin-suna a kasar ta Ethiopia, inda aka saki ‘yan jarida da ‘yan siyasa 11 da ake tsare da su.
Fursunonin da ‘yan jarida da suka zauna a gidan yarin, sun ce an kwashe sauran fursunoni da dama, inda aka mayar da su wasu gidajen yari.
Wannan matakim ya sa masu lura da al'amura tunanin cewa, wannan mataki wata alama ce da ke nuna za a samu sauyi a fagen siyasar kasar ta Habasha.
A ranar biyu ga watan nan na Afrilu, aka zabi Abiy Ahmed a matsayin sabon Firai ministan kasar, bayan da tsohon Firai Minista Hailemariam Desalegn ya yi murabus.
A jawabinsa na karbar mukamin, Ahmed, ya nanata muhimmancin hadin kan kasar ta Ethiopia, yana mai cewa, “daga yanzu, za su rika kallon kowacce jam’iyar adawa a matsayin ‘yan hamayyan siyasa ba a matsayin makiya ba.”
Facebook Forum