Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Akwai Bukatar Yin Sulhu Tsakanin Fadar Shugaban Kasa Da Majalisar Dokoki


Alhaji Abubakar Sani Bello
Alhaji Abubakar Sani Bello

Takun sakar da ke tsakanin fadar shugaban kasar Najeriya, da ‘yan majalisun dokokin kasar na ci gaba da janyo hankulan jama’a, kamar yarda masu nazarin al’amurra suka yi hasashe cewa takun sakar zai iya yin tasiri wajan kawo cikas wajan samae da abubuwan ciyar da kasa gaba.

Gwamnan jihar Neja, Alhaji Abubakar Sani Bello, ya ce duk da yake lamarin ba wata muguwar matsala bace, amma akwai bukatar yin sulhu tsakanin bangarorin, ya kara da cewa idan an sami rashin fahimta kamata yayi a zauna a nemi sasanci da juna.

Akwai kwamiti da shugaban kasa ya kafa wanda mataimakin shugaban kasa yake jagoranta, dan haka zasu kira kowa da kowa domin a zauna a yi sasanci.

Gwamnan wanda ke ci gaba da rangadi a kananan hukumomin jiharsa, a karshen makon nan ya ziyarci kananan hukumomin Bidda da Bako, kuma talakawan yankunan sun bayyana farin cikinsu musamman yadda gwamnan ya ganewa idanunsa irin matsalolin da jama’a ke fama da su, kama daga rashin tsabtataccen ruwan sha, zuwa wutar lantarki.

Alhaji Abubakar Sani Bello, ya sha alwashin samar da ababen more rayuwa a tsakanin al’ummar kananan hukumomin jihar.

Daga karshe gwamnan ya mayar da martani akan wani bidiyo dake yawo a yanar gizo wanda ke nuna lokacin da jama’a ke jifan tsohon gwamnan jihar da duwatsu wanda jama’a da dama suka yi tunanin gwamnan mai mulki yanzu ne.

Mustapha Nasiru Batsari nada karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:58 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG