Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Akwai Bukatar Karatun Ta Natsu Kan Hanyar Shawo Kan Matsalar Wutar Lantarki-Masana


Wutar lantarki ta katse a duk fadin kasar Najeriya
Wutar lantarki ta katse a duk fadin kasar Najeriya

Masaan sun ce akwai bukatar kyakkyawan nazari kan hanyar shawo kan matsalar wutar lantarki a Najeriya, biyo bayan bayanin da Ministan Makamashi Adebayo Adelabu yayi cewa, Najeriya ana bukatar 'yan kasuwa su zuba jarin dala biliyan 10 domin a shawo kan matsalar wutar lantarki a kasar.

Minista Adebayo Adelabu ya ce gwamnatin tarayya ta dukufa wajen ganin an kawo sauyi a fanin samar da wutar lantarki da zai haifar da habbaka tattalin arziki da inganta rayuwar al'umma.

Da yake tsokaci kan batun, kwararre a fanin Tattalin Arziki Shu'aibu Idris Mikati ya ce 'yan siyasa sun jawo wa kasar asara da dama a wannan fanin, inda ya ce samun wutar lantarki ya kasu kashi kashi, saboda haka dole ne Minista Adebayo ya fayyace wa al'umma abinda ya ke nufi da cewa dalar Amurka biliyan 10 zai iya ba wa 'yan kasa wuta har na sa'o'i 24 a rana. Mikati ya ce an kwashi shekaru da dama kan kokarin samar da wutar lantarki, kuma an kashe dalar Amurka fiye da biliyan 40 ko 50, amma ba a shawo kan matsalar ba.

A nashi bayanin, masanin tattalin arziki na kasa da kasa Yusha'u Aliyu ya ce dole ne a duba bunkasar yawan al'umma da cigaban su kafin a fara batun samar da wutar lantarki musamman ma a shiyar Arewa.

Yusha'u ya ce wadannan kudade dalar Amurka biliyan 10, idan an same su za su zama suna da muhimmanci ga tattalin arzikin kasar amma sai an tsaya da gaske, saboda abu ne da za a yi ta yi akai akai domin a baya ma an kashe dalar Amurka biliyan 16 ko fiye, amma ba a samu wadatuwar wutar ba. Yusha'u ya ce matsalar rashin wutar ta fi yawa a Arewa, inda ya bada misali da wasu jihohi da ke gabashin kasar irin su Jihar Abia da ya zuwa yanzu ta yi shekaru 3 tana samun wadatacciyar wuta ta wata hanya daban. Yasha'u ya ce duk kudin nan da aka kashe a baya, megawat dubu 5 ne kadai ake da shi a kasar, kuma komin yawan kudi, karfin watan bai taba wuce haka ba.

A nata bayanin, Hajiya Fatima Abubakar ta ce sauya halayen 'yan Najeriya ne zai kawo canji da zai kai ga samun wutar lantarki ingantacciya ta hanyar gaskiya.

Saurari cikakken rahoton:

Akwai Bukatar Karatun Ta Natsu Kan Hanyar Shawo Kan Matsalar Wutar Lantarki-Masana
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:18 0:00

Dandalin Mu Tattauna

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG