Ministan Lantarki, Cif Adebayo Adelabu ya baiwa kamfani samar da lantaki a Najeriya (TCN) umarnin gaggauta fara aiwatar da shawarwarin kwamitin hukumomi masu ruwa da tsaki, da aka kafa domin magance matsalar yawan durkushewar babban layin wuta a bangaren lantarkin.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da TCN ke roko ga ‘yan Najeriya su fahimci cewar akwai yiyuwar a rika samun katsewar lantarkin daga lokaci zuwa lokaci sakamakon gyaran da aka fara gudanrwa akan babban layin lantarkin.
Umarnin ministan na zuwa ne bayan rahoton da TCN ya fitar na cewar babban layin wutar ya sake katsewa da misalin karfe 11.29 na safiyar jiya Alhamis, 7 ga watan Nuwambar 2024, wacce karuwar da aka samu ta karfin lantarkin daga 50.33hz zuwa 51.44hz ya haddasa shi.
Mashawarcin ministan akan harkokin yada labarai da tsare-tsare, Bolaji Tunji, ya ruwaito ministan na cewar wajibi ne dukkanin fannonin dake da ruwa da tsaki a ma’aikatar su tashi tsaye wajen gaggauta aiwatar da shawarwarin kwamitin, wanda aka gabatar a ranar Laraba, 6 ga watan Nuwambar da muke ciki.
TCN ya gano cewar karuwar da aka samu ta karfin lantarkin cikin sauri ce ta haddasa durkushewar babban layin lantarkin na baya-baya a jiya Alhamis.
TCN ya kara da cewar karuwar karfin lantarkin ta faru ne sakamakon matsalar da aka samu a daya daga cikin kananan tashosinmu, wacce dole aka rufe ta domin dakile ci gaban matsalar.
Dandalin Mu Tattauna