Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira ga Nijeriya ta tsai da rikice-rikicen addini da kabilanci


Wasu da tashe-tashen hankalin Nijeriya ya rutsa da su
Wasu da tashe-tashen hankalin Nijeriya ya rutsa da su

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana damuwa game da yawan

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana damuwa game da yawan rigingimun kabilanci da addinin das u ka addabi yankin tsakiyar Nijeriya, inda hukumomi su ka ce an hallaka wani mutum da ‘ya’yansa bakwai.

Hukumomi sun ce an hallaka wannan iyalin da akalla wani mutum guda, a wani kauye daura da birnin Jos mai fama da tashin hankali.

Mai magana da yawun babban jami’in Majalisar Dinkin Duniya Mai Kula Da ‘Yancin Dan Adam y ace fadace-fadace a yankin tsakiyar Nijeriya sun yi sadadin mutuwar wajen mutane 70 daga watan jiya.

A wata sanarwa ta yau Jumma’a, mai magana da yawun babban jami’in Majalisar Dinkin Duniyar Rupert Colville ya yi kira ga Nijeriya da ta warware tushen rigingimun, musamman ma tsakanin matasan Musulmi da kirista da ke sassan Jos.

Colville ya ce yakamata jami’an tsaron Nijeriya su zamanto masu daukar matakai cikin natsuwa da zarar an sami tashin hankali don kaucewa kara ruruta al’amarin.

Yankin na tsakiyar Nijeriya kusan shi ya raba wannan kasar da ta fi yawan jama’a a Afirka, tsakanin kudancin kasar da Kirista su ka fi yawa, da arewaci da Musulmi ked a yinjaye.

Hukumar kare ‘yancin bil’adama din ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce ainihin dalilan tashin hankalin sun hada da nuna banbanci, da fatara da kuma rikici kan gonaki.

XS
SM
MD
LG