‘Yan sandan Nijeriya sun karfafa matakan tsaro a wasu jami’o’i bayan da su ka sami barazana daga tsattsaurar kungiyar Islamar nan da ta kai wasu munanan hare-hare cikin ‘yan watannin nan.
Hukumomi sun ce kungiyar Boko Haram, wadda sunanta ya samo asali daga akidar cewa “tsarin ilimin yammacin duniya haramun ne,” ta yi barazanar kai hare-hare kan wasu jami’o’i a fadin Nijeriya.
An tsaurara matakan tsaro a harabobin Jami’o’in Ibadan da Benin, wadanda dukkanninsu ke kudancin Nijeriya.
Yakan yi wuya a tantance barazanar Boko Haram saboda yadda shugabancinta da kuma mai magana da yawunta fiye da daya.
A jiya Talata, wata kotu a Nijeriya ta tuhumi wasu mutane 8 da ake ganin ‘yan Boko Haram ne da hannu a jerin hare-haren bama-bamai da harbe-harbe a sassan babban birnin kasar tsakanin watan Maris da Yuli wadanda su ka yi sanadin mutuwar mutane 25.
Kungiyar ta Boko Haram tad au alhakin harin bam din da aka kai a hedikwatan Majalisar Dinkin Duniya da ke Abuja a watan jiya da kuma wanda aka kai a harabar hedikwatar ‘yan sanda a watan Yuni.