WASHINGTON, D.C. - A gabatarwar, Aisha ta bayyana cewa Zahra ta kammala karatun digiri mai daraja ta farko ne a fannin ilimin gine-gine.
“Ina taya Misis Zahra B Buhari murnar kammala karatunki da lambar yabo ta ‘First Class’ a fannin Kimiyyar Gine-gine. Ina muku fatan Alkhairi,” a cewar Uwargidan shugaban kasar a shafinta na yanar gizo yayin da take yada hotunan bikin yaye daliban a shafukan sada zumunta.
Zahra ita ce matar dan Buhari, Yusuf Muhammadu Buhari. Idan za a iya tunawa Yusuf ya auri Zahra ne daga jihar Kano a watan Agusta 2021. Ita ce ta biyu cikin 'ya'yan Sarkin Bichi, Nasiru Ado Bayero.
Wallafa wannan bikin kammala karatu da uwargidan shugaban kasar ta yi ya jawo cece-kuce a shafukan sada zumunta yayin da masu amfani da yanar gizo suka bayyana ta a matsayin ba ta kyauta ba da yin irin wannan a daidai lokacin da aka hana dubban daliban Najeriya zuwa makaranta.
Idan an tuna, jami'o'in gwamnatin Najeriya sun kasance a rufe tun watan Fabrairun 2022 yayin da gwamnatin tarayya da kungiyar malaman jami'o'i (ASUU) ke takun saka.
Kalaman wasu ga Aisha akan shafinta na Facebook:
Dimbo Atiya: “This is insensitive because there are millions of other children at home because of your husband’s incompetence. Let’s call a spade a spade.”
“Wannan rashin hankali ne saboda akwai miliyoyin yara a gida saboda kasawar mijinki. "
Fadima Ibrahim: “Am thoroughly disappointed in you posting this, after knowing full well our students have been at home for months due to your husband’s in competence and nonchalance.”
"Na ji takaici matuka da kika wallafa wannan, bayan kin sani sarai dalibanmu sun shafe watanni suna gida saboda kasawar mijinki da rashin sanin ya kamata."
Benjoe Katangwat: “How do you people feel seeing other children stucked at home with schools closed but still come publicly to show us how your children are graduating elsewhere? Anyway, congratulations to her.”
“Yaya kuke ji kuna ganin wasu yara sun makale a gida tare da rufe makarantu amma har kuna fitowa fili don nuna mana yadda yaranku ke kammala karatunsu a waje? Duk da haka, ina taya ta murna.”