Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Aisha Buhari Ta Bude Wata Cibiyar Kula Da Mata Masu Juna Biyu A Yola


Ya yin da Najeriya ke shirin bikin ranar dimokaradiyya ranar 12 ga watan Yunin shekarar 2019, Uwar gidan shugaban Najeriya Aisha Buhari,ta jagoranci wasu matan shugabanin Afrika zuwa Yola jihar Adamawa, domin bude wata cibiyar kula da mata masu juna biyu da kuma kaddamar da wani sabon shiri na rage talauci ga al'ummar karkara, karkashin hukumar samar da aikin yi ta NDE.

A cikin jawabin ta Aisha Buhari, ta ce “A madadin sauran matan shugabanin Afrika biyar da suka zo don taya Najeriya da yan Najeriya murnar ranar dimokaradiyya, uwar gidan shugaban kasar Ghana Madam Rabecca Akufo Addo,ta ce matan shugabanin kasashen Afrika kan taka rawa ta fannonin ci gaba duk da cewa basu da wani kasafin kudi da akan basu.

Ta kuma yabawa Aisha Buhari, bisa wasu ayyuka da ta kirkiro na ci gaban al'umma. Ita ma a jawabinta, uwar gidan shugaban Najeriya Aisha Buhari, ta ce gidauniyarta ta 'Future Assured' za ta ci gaba da hada kai da sauran cibiyoyi don tallafawa al'umma musamman masu karamin karfi.

Dakta Nasir Ladan, dake zama shugaban hukumar ta NDE a Najeriya, ya bayyana manufar wannan shiri da aka kaddamar a Yola.

Victoria Ajiya, daya daga cikin matan da zasu ci gajiyar wannan shirin ta bayyana farin cikinta inda ta ce “Ina farin ciki da Allah ya yi amfani da uwar mu, wajen samun wannan dama na koyon sana'a don dogaro da kai.

Saurari Rahoton Ibrahim Abdul’Aziz domin jin cikakken bayani:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:13 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG