Majalisar Dokokin jahar Filato ta zabi Abok Izam mai shekaru 33 a matsayin kakakinta.
Abok Izam wanda ke wakiltar Jos ta gabas a majalisar, dalibi ne a bangaren shara’a a jami'ar Jos.
Malam Abok Izam wanda ya sami zuwa majalisar a karkashin jami'yyar APC, wannan shine karonsa na farko a zama dan majalisa.
Malam Emmanuel Zokmal wanda suka yi gwagwarmaya da sabon kakakin wajen ganin matasa sun sami madafun iko, yace zasu ci gaba da bashi shawarwari da kudurori da zasu taimaka wajen inganta shugabanci a jihar.
Shima wani dan jarida, Friday Derwam yace ya kamata Majalisar Dokokin ta tara matasan jihar Filato, don ta fuskanci shawo kan matsalolin tsaro da inganta rayuwar matasa.
Christian Sule wani matashi dake harkar kere-keren injinan sarrafa kayayyakin gona, yace gwamnati ta taimaka wa matasa ta hanyar kimiyya da fasaha.
Ga cikkanken rahoton wakiliyar Muryar Amurka Zainab Babaji.
Facebook Forum