Majalisar dokokin jihar Kadunan Najeriya ta kaddamar da dokar hana wa'azi a ko da yaushe.
Majalisar ta ce wannan doka, don hana tashin hankali ne da kuma kariyar jama'a, saboda akwai wadanda ba masana addini bane amma suna wa'azi, a ko'ina kuma suna tayar da hankalin jama'a.
Tsohon kakakin Majalisar dokokin jihar Kaduna Hon. Aminu Abdullahi Shagali, ya ce dokar ta shafi kowane addini, musulunci da addinin krista.
Ya kara da cewa dama dokar nan ta nan tun 1984, amma yanzu an gyara ta ne don a sake samun zaman lafiya da kwanciyar hankali tsakanin musulmai da krista.
Ga cikkakiyar hirarsu da wakilin Muryar Amurka Yusuf Aliyu Harande.
Facebook Forum