Najeriya ta kwashe kusan shekaru bakwai tana fama da haren-haren kungiyar Boko Haram da ke ta da kayar baya a arewacin kasar musamman a gabashi.
Ayyukan kungiyar ya kai har ga wasu kasashe makwabtan Najeriyar irinsu Jamhuriyar Nijar da Kamaru da Chadi.
Dubban mutane ne suka rasa rayukansu sanadiyar ayyukan kungiyar yayin da miliyoyi suka fice daga mullansu domin kaucewa rikicin.
Yanzu haka kasashen da lamarin ya shafa sun hada rundanar soji ta hadin gwiwa domin tunkarar wannan matsala a yankin kasashen da ke kusa da tafkin Chadi.
Watanni da dama ita ma jihar ta Bauchi ta sha fama da hare-haren kungiyar duk da yake ayyukansu sun fi kamari a jihar Borno da Yobe da Adamawa.
Saurari wannan rahoton wakilin Muryar Amurka Abdulwahab Muhammad domin jin yadda taron addu’oi ya gudana: