Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Boko Haram: Kasar Faransa Ta Taimaka Ma Kamaru Da Kayan Yaki


Shugaba Paul Biya na Kamaru
Shugaba Paul Biya na Kamaru

A wata hobbasa a yakin da ake yi da kungiyar Boko Haram da ke Najeriya, waddda kan ketare kan iyaka ta kai hare-hare a makwabtan kasashe, kasar Faransa ta agaza ma Kamaru da kayan yaki.

Kasar Faransa ta ba wa kasar Kamaru taimakon kayan yaki da su ka hada da motoci 12 masu sulke da riguna suma masu sulke duk a matsayin gudunmowar yaki da Boko Haram.

Jakadiyar Faransa a Kamarun Christele Robinson da ke zaune a Younde ce ta mika gudunmowar a madadin kasar ta Faransa.

Da ya ke amsar kayan yakin a madadin gwamnatin Faransar, Ministan Tsaron Faransa Joseph Beti Assomo ya yaba ma kasar ta Faransa da wannan gudunmowar , ya ce wannan na nuni da irin yadda Faransa ke ba da himma a yaki da Boko Haram, 'yan ta'addan Najeriya mai makwabtaka da Kamaru, wadanda kan kai hare-hare a arewacin Najeriya da makwabtan kasashe.

Ga wakilinmu Garba Awwal da cikakken rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:09 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG