Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Rage Wa Tsoffin Gwamnoni Biyu A Najeriya Zaman Gidan Yari


EFCC
EFCC

Da alamar tsohon gwamnan Jihar Filato Jashua Dariye da tsohon gwamnan Taraba Jolly Nyame za su samu sa'ida yayin da kotun daukaka kara a Abuja ta rage wa kowannan su shekaru biyu a gidan yari

Kotun daukaka kara a karkashin mai shari'a Steven Adah ya rage wa tsoffin Gwamnoni biyu wa'adin shekarun da za su yi a fursina.

Gwamnonin su ne tsohon Gwamnan Jihar Filato Joshua Dariye da Jolly Nyame na Jihar Taraba.

Joshua Dariye zai shafe shekaru 11 a maimakon 14, shi kuwa Jolly Nyame zai yi shekaru 12 a maimakon 14, sannan kuma zai mayar wa Gwamnati Taraba kudi wuri na gugar wuri har Naira miliyan dari hudu da casa'in da biyar.

Barista Jumboh Festus, lauyan Joshua Dariye, ya ce za su yi nazarin hukuncin da kotu ta yanke sannan kuma za su ba wa wanda su ke karewa shawara, idan ya ba mu umarnin mu sake daukaka kara, za mu bi umarnin nasa. saboda ba mu gamsu da shari'ar ba domin shi wanda mu ke karewa bai aikata wannan laifi da ake zargin sa da shi ba.

Ga wakiliyar mu Medina Dauda da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:18 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG