Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Sandan Kasar Myanmar Sun Raunata 'Yan Rohinja Mutum 4


Yanzu haka yan sandan kasar Myanmar sun harbi wasu musulmai yan Rohinja guda hudu a wani sansanin yan gudun hijira da ke yammacin jihar Rakhine.

Rahotanin harbe-harbe da ake zargin ‘yan sandan kasar Myanmar da yi, a wani sansanin 'yan gudun hijirar jinsin Rohinja a jihar Rakhine ya janyo damuwa daga jami’an Majalisar Dinkin Duniya.

Knut Ostby, shugaban hukumar bada taimakon agaji na Majalisar Dinkin Duniya, ya rubuta a shafinsa na Twitter, cewa ya damu matuka akan rahotannin harbe-harbe da ya ji anyi a sansanin Ah Nauk Ye da ke tsakiyar jihar Rkhine.

Kasar Myanmar dai tana da mutane da dama da su ka guje wa tashe tashen hankula tun shekarar 2012, da su ke zaune a sansanoni 'yan gudun hijira.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ambato wasu shedu da suka ce ‘yan sandan Myanmar sun yi harbi, da kuma raunata 'yan Rohija mutun hudu a jiya Lahadi, yayin da suke tsare da wasu mutane biyu da su ke zargin su da fitar da mutane ta barauniyar hanya daga cikin sansanin ‘yan gudun hijirar, da ke yammacin jihar Rakhine.

Duk da haka ‘yan sandan sun fadawa kamfanin dillancin labarai cewa 'yan Rohinja sun zagaye su ne da takubbai kuma suna jifansu da duwatsu.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG