Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Adamawa: An Fadakar Da Dalibai Kan Yadda Za Su Gane 'Yan ta'adda


Bitar fadakarwa a jihar Adamawa
Bitar fadakarwa a jihar Adamawa

Biyo bayan irin matsalar ta’addanci da jihohin arewa maso gabashin Najeriya suke fuskanta, ya sa cibiyar tattara bayanai da ci gaba, wato Centre for Information Technology and Development, CITAD, ta shirya bitocin fadakar da daliban manyan makarantun gaba da sakandare da a jihar Adamawa kan hanyoyi kariya.

Kamar yadda alkaluma ke nuna wa, dalibai da malamai da dama ne suka rasa rayukansu ta sanadiyar hare-haren Boko Haram musamman a jihohin arewa maso gabas.

Wannan batu ya sa a yanzu cibiyar tattara bayanai da ci gaba ta Centre for Information Technology and Development (CITAD), ta fara fargar da al’ummomin arewa maso gabas wato North East Regional Initiative (NERI), ta hanya shirya bitoci domin zaburar da dalibai sanin hanyoyin dakile ayyukan ta’addanci a manyan makarantu.

Da yake jawabi wajen tarukan bitan a jihar Adamawa inda aka gayyato dalibai daga jami’o’i da manyan kwalejoji a jihar don tafka muhawara, Mr. Yunus Zakari, da ke zama babban daraktan cibiyar tra CITAD, ya ce dole a ilmantar da dalibai don kare rayuka.

‘’Dole ake shirya irin wannan muhawara domin dalibai su san illoli da kuma hanyoyin dakile ayyukan ta’addanci a manyan makarantun mu.’’

Umar Sale Dan Yaro wani dalibi da ya halarci bitar, ya ce ayyukan ta'addanci na ta da hankali saboda yana iya faruwa da kowa.

Ya yi kira ga dalibai da su rika yin hankali da wadanda suke cudanya da su.

Wani na iya zuwa da suna shi dalibi ne amma ya zama wani abu daban, inji shi.

Ya kara da cewa akwai muhimmanci kowace makaranta kafin ta dauki sabbin dalibai ta rika shirya irin wannan bitar domin fadakar da su akan illolin ta’addanci.

Shi ma Adamu Yahaya daga kwalajin fasaha na Adamawa ya ce mutum ya kula da wadanda yake makaranta da su saboda akwai dabi’u daban-daban a kowace makaranta.

A watannin baya,kwalejin kimiyya da fasaha ta jihar Adamawa ta taba fuskantar harin ta’addanci inda aka ta da bom a wani massalaci da ke kwalejin lamarin da ya janyo asarar rayuka.

Malama Sa’adatu Aminu Barkindo,malama a kwalejin ta ce dole a hada kai don fadakar da dalibai.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:13 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG