A birnin Abuja 'yansanda sun kafa shinge domin gangamin da 'yan gwagwarmayar kwato 'yan matan Chibok da aka sani da suna Bring Barl Our Girls da suka yi kokarin shiga fadar shugaban Najeriya ta Aso Rock don sadawa da shugaban a ranar cika kwanaki dubu daya da sace 'yan matan.
'Yan kungiyar na dauke da hotunan sauran 195 da har yanzu suna hannun 'yan Boko Haram tare da kiran lallai sai an ganosu a kubutar dasu.
Masu fafutikar sun amince da kokarin da gwamnati tayi amma suna kira ta kara kaimi domin a kawo karshen gwagwarmayar don kowa ma ya huta.
'Yan gwagwarmayar na tambayan inda 'yan matan suke bayan ikirarin tarwatsa tungar 'yan Boko Haram din a dajin Sambisa da sojoji suka yi saboda an kyautata zaton a dajin ne 'yan matan suke.
Mai magana da yawun kungiyar Bring Back Our Girls tace ba'a barin kafofin labaru masu zaman kansu su san ainihin gaskiyar abubuwan dake faruwa saidai abun da sojoji da gwamnati suka ce.
Kakakin kungiyar Emmanuel Shehu yace tun farko shugaban Najeriya yace idan ba an kwato 'yan matan Chibok ba to ba'a kare yaki ba. Saboda haka ikirarin cewa an gama da kungiyar Boko Haram ba gaskiya ba ne, inji Emma Shehu.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.