Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari Ya Yi Magana Da Mahaifiyar Leah Sharibu Karon Farko


Rabecca Sharibu, Mahaifiyar Leah Sharibu
Rabecca Sharibu, Mahaifiyar Leah Sharibu

Karon farko, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi magana da Madam Rebecca Sharibu, Mahaifiyar Leah Sharibu dalibar makarantar sakandaren 'yanmmata ta Dapchi daya tilo da ta rage a hannun kungiyar Boko Haram, bayan watanni bakwai da sace ta.

A cikin sakon da ya wallafa a shafinsa na twitter, shugaba Buhari yace

"Yau nayi magana da Mrs Rebecca Sharibu, domin in jadada aniyarmu ta dawo da 'yarta gida lami lafiya. Dukan 'yan Najeriya suna yiwa iyalin Sharibu da kuma iyalan dukan wadanda har yanzu suke tsare addu'oi. Zamu yi iyaka kokari mu dawo da su".

"Today I spoke with Mrs Rebecca Sharibu, to reiterate our determination to bring her daughter Leah back home safely. The thoughts & prayers of all Nigerians are with the Sharibu family, & the families of all those still in captivity. We will do everything we can to bring them back" @Mbuhari

Shima a nasa shafin na twitter, kakakin shugaba Buhari Garba Shehu ya buga cewa,

" Ranar Laraba shugaba Muhammadu Buhari ya yi magana da Mrs Rebecca Sharibu, mahaifiyar dalibar makarantar sakandaren Dapchi da kungiyar 'yan ta'addan Boko Haram ta sace, ya kuma bada tabbacin cewa, gwamnatinsa zata yi iyakar kokari ta dawo da ita gida."

"President Muhammadu Buhari, Wednesday, spoke with Mrs Rebecca Sharibu, mother of the Dapchi Secondary schoolgirl, Leah, who had been kidnapped by Boko Haram terrorists, and assured her that his administration will do everything it would take to bring her daughter back home." The President consoled the Sharibu family and assured the parents that the Federal Government would do its utmost for the safety and security of their daughter. "I convey my emotion, the strong commitment of my administration and the solidarity of all Nigerians to you and your family as we will do our best to bring your daughter home in peace and safety, President Buhari told her. He assured the mother that his heart was with her family, as that of the entire nation which continues to pray for the safe return of our daughter, Leah.” @GarbaShehu

sai dai mutane da dama sun yi ta kushewa wannan sanarwar da suka danganta da siyasa da neman goyon baya a zaben shekara ta dubu biyu da goma sha tara, kasancewa babu wanda ya tuntubi iyayen ko bayan maido da sauran daliban da kuma fitar da muryar Leah .

A cikin makonni biyu da suka shige aka rika fitar da rahotanni masu karo da juna dangane da cewa mahaifiyar Leah da kuma wadansu 'yan fafatuka sun shigar da kara suna neman gwamnatin tarraya ta dawo da Leah da kuma sauran 'yammatan sakandaren Chibok dari da goma sha biyu da suka rage a hannun kungiyar Boko haram. Rahotannin sun kuma yi nuni da cewa, yayin ganawarta da wata kungiya mai zaman kanta cikin wannan makon, mahaifiyar Leah tayi kira ga shugaba Muhammadu Buhari kada ya bari kungiyar Boko Haram ta kashe 'yarta biyo bayan barazanar da kungiyar tayi kwananan nan cewa, za a yi da na sani, idan aka yi watsi da bukatar da suka gabatar.

A cikin wannan makon ne har wa yau wata hadakar kungiyoyi, tare da hadin guiwar kungiyar lauyoyi da kuma kiristoci suka gudanar da wani gangami a birnin Tarayya Abuja inda suke kira ga gwamnati tarayya kada ta bari kungiyar Boko Haram ta kashe Leah, yayinda darikar ECWA ta yi azumi da addu'oi na kwanaki uku makon jiya domin Leah, da kuma wadanda kungiyar Boko Haram ke rike da su. Ana kuma gudanar da irin wadannan addu'oi a majami'u da dama a wadansu kasashen duniya.

Dukan wadannan na faruwa ne bayan fitar da wani faifai da aka yi ranar ishirin da takwas ga watan Agusta inda aka ji Leah tana kira ga gwamnatin tarayya ta yiwa Allah ta gaggauta daukar matakan sakinta.

Za a iya tuna cewa, an sace Leah Sharibu ne ranar goma sha tara ga watan Fabrairu wannan shekarar, tare da wadansu dalibai mata dari da goma a makarantar Sakandaren 'yammata ta Dapchi, 'yan kimanin shekaru 15-19, da karfe biyar da rabi na maraice, ranar 21 ga watan Maris, kuma kungiyar Boko Haram ta maido da 'yammata dari da hudu. Bisa ga bayanan daliban, abokansu biyar sun rasu sakamakon azaba da suka sha lokacin da aka sace su, suka kuma bayyana cewa, kungiyar kuma taki sakin Leah ne sabili da taki Musulunta. Iyayen Leah sun kuma bayyana cewa, duk kokarin da suka yi tunda da aka dawo da sauran 'yammatan, na neman ganawa, ko neman bayani daga gwamnati ya cimma tura, sai zuwa jiya da shugaba Buhari yi magana da Leah kamar yadda aka wallafa.

Saurari bayanin Garba Shehu

Buhari ya yi magana da mahaifiyar Leah Sharibu-2:00"
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:35 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG