Mustapha Mohammad Hausawa – Furodusa wanda ya fi maida hankali ko kwarewa a fannin “Documentaries” wato shirye-shirye na musamman da ake shafe dogon lokaci kafin a hada shi a kuma saka shi a gidajen talabijin.
Kamar yadda kowanne dan Adam idan ya tashi yana da wani abu da yake son cimma, ya Allah ta fannin kawo gyara ga al'ummarsa, wanda shima Mustapha hakan ne yaba shi sha’awar harka ta fim ganin cewa akwai matsaloli a zamantakewar rayuwar yau da kullun.
Mustapha, wanda yafi maida hankali wajen gabatar da shirye shiryen documentary wato wani shiri na mussaman da ya dangacin wani al’amari da ke damun alumma baki daya. Ko tarihin yadda wasu abubuwa suka gudana a rayuwa.
A ta bakinsa mafi yawan fina-finai ko documentaries da yake aiki akansu mafi akasari akan matsalolin zamantakewa ne da tabarbarewar al'ada, mussaman idan aka danganta da matasa.
Daga karshe Mustapha, ya bayyana cewa wasu daga cikin kalubalen da suke fuskanta sun hada da rashin bada hadin kai daga wasu abokan aiki, mussaman ma a farkon shigar mutun kafin a san kwarewarsa.
Facebook Forum