Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Abin Da Buhari Ya Ce Kan Kisan Dalibar Da Ake Zargi Da Yin Sabo A Sokoto


Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari (Hoto: Fadar shugaban kasa)
Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari (Hoto: Fadar shugaban kasa)

“Labarin kisan matashiyar dalibar da dalibai suka yi abin damuwa ne, wanda ke bukatar kwakkwaran binciken da ba zai nuna bangaranci ba, kan dukkan abin da ya faru.”

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya nemi da a kai zuciya nesa dangane da kashe wata dalibar kwaleji da wasu dalibai suka yi a jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin kasar, bayan da aka zarge ta da yin batanci ga Annabi Muhammad (SAW.)

Cikin wata sanarwa da Kakakin Buhari Malam Garba Shehu ya fitar a ranar Juma’a, shugaban ya ce ana gudanar da bincike kan lamarin.

Shugaban na Najeriya ya ce, Musulmi a duk fadin duniya, na da fatan su ga ana mutunta dukkan annabawa da suka hada da Annabi Isa Alahissalam (Jesus Christ) da Annabi Muhammad (SAW.)

“Amma wadanda suka wuce gona da iri, kamar abin da ake zargin ya faru a wannan lamari, hukuma ba ta amince kowa ya dauki doka a hannu ba.”

“Babu wanda yake da hurumin ya dauki doka a hannu a wannan kasa, ta da hankali, bai taba zama maslaha ga kowacce irin matsala ba.” Shugaba Buhari ya ce cikin sanarwar.

Shugaban ya kuma yi Allah wadai da kisan dalibar mai suna Deborah Samuel, wacce ke aji na biyu a Kwalejin Ilimin ta Shehu Shagari da ke jihar.

“Labarin kisan matashiyar dalibar da dalibai suka yi abin damuwa ne, wanda ke bukatar kwakkwaran binciken da ba zai nuna bangaranci ba, kan dukkan abin da ya faru.

“Baya ga haka, malaman addini suna wa’azin cewa, mutum ba shi da hurumin ya yankewa wani hukunci kan wani abu da ya aikata.

“Buhari na kira ga kafafen yada labarai da su tantace labaran da za su watsa tare da yin kira ga jama’a da su kwantar da hankulansu yayin da ake gudanar da bincike kan musabbabin wannan al’amari.” In ji sanarwar.

Shugaban na Najeriya ya kuma mika sakon ta’aziyyarsa ga iyayen dalibar tare da yi wa wadanda suka ji rauni fatan samun lafiya.

A ranar Alhamis ne aka kashe Deborah, bayan da aka zarge ta da furta kalaman batanci ga fiyayyen halitta, lamarin da ya sa wasu matasa suka kashe ta.

Bayanai sun yi nuni da cewa hukumomin tsaron makarantar sun yi kokarin kubutar da dalibar a lokacin da aka far mata, amma lamarin ya ci tura bayan da matasan daliban suka fi karfinsu.

Tuni dai gwamnatin jihar ta Sokoto ta ba da umarnin rufe makarantar tare da jigbe jami’an tsaro a farfajiyarta.

Rundunar ‘yan sandan jihar ta Sokoto ta fada a cikin wata sanarwa da ta fitar bayan aukuwar lamarin cewa, an kama mutane biyu da ake zargi na da hannu a wannan kisa.

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG