Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hamas Ta Nada Yahya Sinwar A Matsayin Sabon Shugabanta


Israel Palestinians
Israel Palestinians

Sinwar ya maye gurbin Isma’il Haniyeh wanda aka halaka a Iran a makon da ya gabata a wani harin sama da ake zargin Isra’ila ce ta kai.

Kungiyar Hamas ta Falasdinu ta sanar da nada Yahya Sinwar a matsayin sabon shugaban kugiyar.

Sinwar shi ne mutumin da ake zargi da kitsa harin ranar 7 ga watan Oktoba da kungiyar ta kai cikin Isra’ila.

Sinwar ya kasance mutumin da Isra’ila ta fi nema cikin jerin mutanen da take kokarin halakawa a kokarin da take yi na kassara kungiyar da shugabanninta tun bayan harin 7 ga watan Oktoba.

Ya maye gurbin Isma’il Haniyeh wanda aka halaka a Iran a makon da ya gabata a wani harin sama da ake zargin Isra’ila ce ta kai.

Sabanin Haniyeh da ke gudun hijira a Qatar tsawon shekaru a lokacin da yake raye, Sinwar na zaune ne a yankin na Zirin Gaza da ake gwabza fada.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG