BIRNI N'KONNI, NIGER - Kasar Japan ta tallafa wa Jamhuriyar Nijar da buhunan shinkafa dubu 74 da za a sayar a sassan kasar don rage radadin hauhawar farashin abinci, haka kuma kasar zata iya amfani da kudin shinkafar domin gudanar da ayyukan ci gaban kasa.
Albarkacin yarjeniyoyin da kasashen Nijar da Japan suka cimma a 1999, musamman ta taimakon juna da kayan abinci ya sa kasar Japan tallafa wa jamhuriyar Nijer da Tan 3,700 da na shinkafa, kwatankwacin buhunan shinkafa dubu 74 da kudinsu ya kama billiyon 2 na CFA.
Manufar taimakon shi ne rage wa talakawan kasar radadin zafin rayuwa, duba da cewa ba a kai ga sabuwar cimakar karshen daminar bana ba, da kuma saukaka hauhawar farashin kayan masarufi a cikin kasuwannin kasar tunda bayan hatsi shinkafa ce dangin abincin da ‘yan Nijer suka fi ci.
Idan hukumomin kasar suka sayar da shinkafar za su saka kudin cikin wani asusun kasashen biyu na bai daya da ake kira K.R don tunkarar matsalolin da ka iya bijirowa.
Adu Ibrahim, shi ne magatakardan ofishin ministan harkokin kasuwanci na jamhuriyar Nijer, ya ce saka irin wadannan kudin a cikin asusun na K.R a ‘yan shekarun baya - bayan nan, ya bai wa hukumomin kasar damar tunkarar wadansu matsaloli masu zafin gaske, kamar tattalin abinci a cikin rumbunan gwamnati da kudinsu ya kai CFA biliyan 1 da miliyon 450, da ma sayen abincin da a ke nomawa a kasar da ya kai kudi CFA biliyon 1 da miliyan 485 don tanadin abincin agazawa talakawa da gaggawa da a ke ajiyewa a rumbun gwamnati mai suna OPVN.
A nasa bangaren jakadan Japan a Nijer Ikkatai Katsuya da ke zama a kasar Ivory Coast, yana mai cewa kasar Japan zata ci gaba da yin irin wannan kokari don Nijer, kuma ya kamata Nijer ta kara daukar matakai wajan saukaka shigo da kayayyakin da ake kai mata, ta hanyar saukaka harajin shigo da kaya da sauran su.
Bayan haka Nijar ta kara kaimi da hanzari domin kudaden da za su fito ta hanyar sayar da wannan shinkafar su amfani wadanda aka bada tallafin dominsu.
Sai dai a cewar Jafaru Sarkin Shanu wani dan fafutikar kare hakkokin talakawan kasar, ba bada taimako domin a sayar wa talakawa shinkafar ba, amma a gani a kasa. Yana kuma fatan wasu ba zasu karkata tallafin zuwa wani wuri ba.
Saurari rahoton Haruna Mamane Bako.