Kamar yadda rahotanni ke cewa ,yanzu wani sabon tashin hankali ne ya sake barkewa a tsakanin makiyaya da kuma kuteb tsakanin Takum da Ussa ,wanda kawo yanzu kuma ba’a tantance alkalumman rayukan da aka kashe ba.
Wannan sabon fadan na zuwa ne a kasa da sa'o'i 44 da kammala wani taron sasantawan da aka yi karkashin wata tawagar da gwamnatin jihar ta tura domin shiga tsakani ,kamar yadda wani dan yankin da bai son a ambaci sunansa ya shaida.
Da yake tabbatar da barkewa wannan sabon rikicin shugaban hadakar kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah Sahabi Mahmud Tukur yace kawo yanzu akwai wasu makiyayan da ba’a san inda suke ba,baya ga shanun dake daji.
Gwamnan jihar Taraba,Akitet Darius Dickson Isiyaku ya nuna bacin ransa game da tashin hankalin inda ya danganta matsalar rashin hanya da cewa shike hana isa ga kauyukan da lamarin ke faruwa.
Gwamnan ta bakin hadiminsa ta fuskacin harkokin siyasa Abubakar Bawa ya bayyana matakan da ake dauka don gano bakin zaren magance tashin tashinan.
Kawo yanzu tuni aka tura jami’an tsaro don kwantar da rikicin,kamar yadda kakakin rundunan yan sandan jihar ASP David Misal ke cewa.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani.
Facebook Forum