Kwamitin warware tashe-tashen hankula da samar da dawamammiyar zaman lafiya tsakanin al’umomin Shomo da Jole na yankin tafkin Marimi a karamar hukumar Lau dake jihar Taraba ya bada tabbacin za a samu masalaha ga rigingimun da jihar ke fama da ita baki daya.
Mataimakin gwamnan jihar Taraba Injiniya Haruna Manu, kuma shugaban kwamitin da mambobinsa da suka kai ziyara yankin tafin ya bada tabbacin haka lokacin da ya ke bayanin dalilin ziyararsu wanda ya ce gwamnati ba ta jin dadin sake afkuwar rigingimun musamman na baya-bayan nan da ya yi sanadiyyar hasarar rayuka da dimbin dukiyoyi.
A baya dai gwamnatin jihar Taraba ta sha nada irin wadannan kwamitocin ba tare da ta sami nasarar magance matsalar ba wanda kwamishinan yada labarai kuma mamba a kwamitin Barrister, Anthony Danburam ya ce zasu yi wa dukkan bangarorin da basu ga macijin da juna adalci ba tare da fifita wani bangare ba, nuna tsoron Allah tare da la’akari da dangantaka ta zamantakewa tsakanin al’umomin biyu.
Shi ma sarkin Lau Alh, Abubakar Sadiq Danburam mamba a kwamitin ya bukaci al’umomin Shomo da Jole su kai zuciya nesa yana me cewa suna sane yankin ya jima yana fama da rikici kan tafkin Marimi wanda ba za su kyale yana ci gaba da faruwa ba. Basaraken yace abinda ya kamata shine jama’a su daina daukar makamai suna yiwa juna lahani.
Tashe-tashen hankula na yankin tafkin Marimi ya samo asali ne sama da shekara talatin da suka gabata kan mallakar tafkin mai dimbin albarkatu na kifi da ruwa na noman rani. Sau biyar ke nan ake samu rikici tsakanin al’umomin da ya haddasa hasarar rayuka da dukiyoyi na miliyoyin Nairori.
Facebook Forum