WASHINGTON, DC —
Dangane da abubuwan da suka faru a bayan zaben 2011, daya jawo rasa rayuka, yasa Gidan Radiyon muryar Amurka, tare da hadin gwiwar hukumar zabe suka gudanar da wani taro na masamman domin kara fadakar da matasa, kan gudanar da zabe cikin kwanciyar hankalin da lumana.
A zauran taron hukumar zabe wato {INEC} tayi bayani dagane da yadda za’a tantance masu jefa kuri’a, da kuma tabbatar da ganin cewa mutun bai iya jefa kuri’a, fiye da sau daya ba.
Kungiyoyin matasa da daban-daban da kuma wakilai daga jam’iyyu daban-daban ne suka halarci taron, da zammar ganin cewa an gudanar da zabe cikin lumana.
##caption:Matasa a Zauren Taro##