Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Karo Na 2 Facebook Ya Dakile Manhajar Tambaya A Shafin Shi


Shafin zumunta na Facebook a karon na biyu ya dakile wata manhaja a shafin sa, ita dai manhajar wasa kwakwalwa ‘Quiz app’ wasu bata gari sunyi amfani da ita wajen satar bayanan jama’a da kuma amfani da datar su ta shiga yanar gizo ba bisa ka'ida ba.

A jiya Laraba ne kamfanin ya dauki wannan mataki akan kamfanin myPersonality app, biyo bayan gano cewar kamfanin ya dauki bayanan mutane don saidawa kamfanonin bincike da wasu kamfanoni da basu da tsarin kare bayanan mutane masu inganci.

Kamfanin yace zai bayyana ma mutane da wannan matsalar ta shafa a duk lokacin da aka taba musu datar su ba bisa ka’ida ba, wannan shine karo na biyu da kamfanin ya taba daukar mataki irin wannan, bayan dakile manhajar wani kamfani da yayi, wanda yake amfani da bayanan jama’a don cinma wani buri na siyasa.

Kamfanin na myPersonality ya bayyana cewar ai wannan manhajar tana aiki tun kamin shekarar 2012, amma mai yasa kamfanin na Facebook bai dauki matakin dakile manhajar ba tun a wancan lokacin ba sai yanzu.

An dai kirkiri manhajar tun a shekarar 2007 wadda aikin manhajar shine ta tambayi mutun wasu bayanan sa kamin bude shafi a yanar gizo na Facebook, wanda Mr. David Stillwell ya kirkira.

Binciken kamfanin Cambridge Analytical ya kara wayema kamfanin na Facebbok ido wajen ganin ya dauki kwararan matakai wajen kare bayanan jama’a. Hakan yasa kamfanin Facebook baya wasa da duk wata magana da ta shafi bayanan sirrin jama’a.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG