Shugaban Amurka Donald Trump, ya bayyanar da cewar babban hadari ne ga kamfanonin sadarwa kamar su Facebook da Twitter, su dinga rufe shafukan mutane, dake bayyanar da ra’ayoyin su. Shugaban yayi wannan maganar ne a lokacin da yake zantawa da kamfanin dillancin labarai na Reuters.
Kamfanonin sada zumunta na yanar gizo dai na fuskantar matsin lamba daga majalisar dokokin Amurka, musamman wajen bibiyan wasu bayanan farfaganda da ake watsawa ta kafofin. Shugaba Trump dai nada mabiya a shafin shi na Twitter sama da mutane milliyan hamsin da uku 53.
Shugabana dai kanyi amfani da shafin nashi wajen bayyanar da kudurorin gwamnatin shi, da bayyanar da wasu ra’ayoyin shi, kana yana amfani da dammar wajen kaima ‘yan adawa hari na magana. Ana kallon wannan matakin da shugaban yake dauka na amfani da shafin Twitter a matsayin babban cikas ga gwamnatin shi.
A ranar 18 ga wannan watan ne shugaban yayi kausasan maganganu akan kafofin sadarawar yanar gizo, inda yake cewar shafukan na nuna wariya musamman ga ‘yan jam’iyar shi da ma wasu masu ra’ayin rikau, inda ake danne musu hakkin su, ya bayyanar da haka ne a wasu rubuce rubucen shi a shafin nashi na Twitter.
Facebook Forum