Duka sassan biyu suna zargin juna da tada fitinar wacce tayi sanadiyyar hasarar rayuka daga duka sassan biyu. Zuwa yanzu dai babu adadin mutane d a suka halaka sakamaon wannan rikici.
Mazauna yankin suna kira ga gwamnatin jihar ta sassauta dokar hana fita d a ta kafa saboda mutane suna fuskanatar karancin abinci da wasu muhimman kayan more rayuwa. Wannan dokar tuni ta hana mutane zuwa ayyuakan ibada ranar jumma'a da kuma lahadi.
Injiniya Sa'ad Bako mai gyaran na'ura mai kwakwalwa yace lamarin yana da dan sauki a unguwarsu, domin suna fita su zauna idan suka hangi jami'an tsaro sai su koma cikin gida. Yace ba haka lamarin yake a wasu unguwanni ba.
Mr. Joel shugaban matsa na kungiyar CAN ya yaba d kafa dokar hana fitar, duk haka shi ma yana kira da gwamnati ta sassauta dokar.