Domin samun cikkaken bayani dangane da lamarin da ya faru a garin Yadin Buni abokin aiki Sahabo Imam Aliyu ya zanta da wani mazaunin garin. Ta bakin mutumin wanda ya fita daga garin zuwa Damaturu ya ce har yanzu ana zaman dar dar a garin sabili da harbe-harben da aka yi daren jiya. Mutane sun kwana babu barci tare da tunane da yawa. Harbe harben kusan duk cikin garin aka yi.
Wuraren da suka fi samun matsala su ne inda sojoji suke domin an kona gidan da suke ciki.Yan bindigan da suka shigo garin su ne suka kai hari wurin da aka tsugunar da sojoji.A aika-aikar an samu rashin rayuka har da babban dan wani mutum da aka ce ya yi fice wurin taimakon mutane. Wasu kuma sun samu raunuka.
Jami'an tsaro sun bazu a gari suna duba wuraren da aka kai hari suna kuma yin aikin bincike. Kodayake babu mutane dake barin garin amma kowa ya zauna gidansa domin rashin sanin tabbas.
Ga karin bayani.