Cikin 'yan takarar da aka tantance har da bakwai da ba su cika sharuddan shiga takarar ba.
Hakan dai na nufin cewa mambobin jam’iyyar APC 182 ne suka sami nasarar tsallake aikin tantancewar da ya kammala a jajibirin ranar babban taron, wanda ake kan gudanarwa a dandalin Eagle Square.
Gwamna Masari ya bayyana hakan ne a wata hira ta musamman da ya yi da wakiliyar Sashen Hausa na muryar Amurka a birnin tarayya, Abuja gabanin taron na yau asabar 26 ga watan Maris.
A cewar gwamna Masari, cikin dalilan da ya sa wasu ‘yan jam’iyyar da suka mika takardar neman takara ba su sami nasarar tsallake aikin tantancewar ba, har da rashin cika sharuddan shekarun da kundin tsarin jam’iyyar ya tsaida na neman wasu mukamai.
Gwamna Masari ya kara da cewa wadanda ba su cancanci tsayawa neman takarar ba ba su tafi da fushi ba sakamakon yadda suka fahimci dalilan da su ka hana su tsallake aikin tantancewar. Saidai duk wanda ya zo neman abu bai samu ba, ba zai ji dadi ba.
Bayan kammala aikin tantancewar, an sami wasu koke-koke a rubuce, amma jam’iyyar ta bi kadunsu kuma dalilan ba su isa hujjar hana wani da ya cancanta tsayawa neman takara ba, in ji Gwamna Masari.
An dai ga 'yan takara na tururruwa zuwa masaukin shugaban kwamitin aikin tantance 'yan takarar mukamai daban-daban na jam’iyyar APC don karban takardar shaidar tsallake aikin tantancewar da maraicen ranar Juma’a a yankin Asokoro dake Birnin T Tarayya Abuja.
Saurari cikakken rahaton cikin sauti: