Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Katsina Za Ta Maka Hukumar Kwastan A Kotu


KATSINA: Gwamnan Katsina Bello Masari.
KATSINA: Gwamnan Katsina Bello Masari.

"Lokaci ya yi da hukumar ta kwastan za ta gane cewa yadda jami’anta ke aiki a jihar Katsina ya saba doka, kuma ba za’a lamincewa haka ba."   

Masu fashin baki sun dade suna sharhi akan ayukan jami’an hukumar yaki da fasa kwabri, wato kwastan a jihar Katsina da ke kan iyakar Najeriya da kasar Jamhuriyar Nijar, tun lokacin da gwamnatin Najeriyar ta saka haramci akan shigowa da kayayyakin abinci, musamman shinkafa.

To sai dai da alama gwamnatin jihar ma ta soma fusata da ayukan na jami’an kwastan a jihar, biyo bayan lamarin da ya faru baya-bayan nan, da yayi sanadiyyar mutuwar akalla mutane 10 da basu ji ba basu gani ba.

Rahotanni sun bayyana cewa a cikin makon da ya shige, jami’an na kwastan suka kade mutane da dama da motarsu, a yayin da suke kokarin bin wani da suke zargi ya dauko shinkafa a motarsa, a yankin karamar hukumar mulkin Jibiya.

Shaidun gani da ido dai sun tabbatar da cewa jam’ian suna gudu sosai da tukin ganganci da motar ta su a cikin jama'a, sa’adda suka kade mutane da dama, inda 10 suka rasu, wasu kuma da dama suka sami raunuka.

A yayin da ya kai ziyarar jaje ga iyalan wadanda lamarin ya rutsa da su a Jibiya, gwamnan jihar Aminu Bello Masari ya sha alwashin daukar matakin shari’a, domin bin kadin hakkokin wadanda suka mutu da wadanda suka sami rauni sakamakon halayyar ta jami’an na kwastan.

Ya fadawa iyalan mutanen cewa sam ba za’a bari hakkokinsu su tafi a banza ba. “Gwamnati na nan tana shirin daukar dukkan matakan da suka dace na shari’a, domin karbowa iyalan marigayan hakkokinsu, har ma da na wadanda suka sami raunuka” in ji Masari.

Ya kara da cewa tuni da aka tuntubi kwararru a fanni shari’a, domin su ba da shawarar yadda za’a tunkari al’amarin, da kuma tabbatar da ya gudana cikin sauri ba tare da wani tsaiko ba.

Akan haka gwamnan ya gargadi iyalan wadanda lamarin ya rutsa da su, da kada su karbi kowace irin kyauta ko toshiyar baki daga hukumar ta kwastan, domin yin hakan kan iya kawo cikas ga fafutukar neman hakkin marigayan da kuma wadanda suka ji rauni.

Gwamna Masari ya kara da cewa lokaci ya yi da hukumar ta kwastan za ta gane cewa yadda jami’anta ke aiki a jihar Katsina ya saba doka, kuma ba za’a lamincewa haka ba.

XS
SM
MD
LG